✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An nada dan ‘Shugaban Kasar Nijar’ Ministan Mai

Mahamane Sani shi ne sabon Ministan Mai da Makamashi na Jamhuriyar Nijar

Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum ya nada Mahamane Sani Mahamadou, dan Shugaba Mahamdou Issoufou Ministan Mai da Lantarki na Kasar.

Mahaifin Mahamane Sani Mahamadou shi  ne Shugaban Kasar da ya mika mulki ranar Juma’a ga Bazoum, wanda tsohon na hannun damansa ne kuma Ministansa na Harkokin Cikin Gida.

Sunan Mahamane Sani Mahamadou na daga cikin ministoci 33 da Firai Minista ya gabatar wa Shugaba Bazoum domin amincewarsa, a cewar Sanarwar da Sakataren Gwamnatin Kasar, Abdou Dan Galadima ya fitar.

A ranar Asabar, Shugaba Bazoum ya sanar da nadin Ouhoumoudou Mahamadou a matsayin Firai Minista, wanda kuma ke da alhakin kafa Majalisar Ministocin Kasar.

Ouhoumoudou Mahamadou shi ne Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa kuma Ministan  Ma’adinai, Makamadi, Kasuwanci da Kudade a lokacin Gwamnatin Shugaba Mahamadou Issoufou.

Zaman Majalisar Ministocin Shugaba Bazoum na farko, ranar Alhamis, 8 ga Afrilu, a 2021. (Hoto: @Mohamed.Bazoum)

A ranar Alhamis, 8 ga Afrilu, 2021, Bazoum ya jagoranci taron farko na Majalisar Ministocin Kasar.

Sauran nade-naden sun hada da:

Ministan Tsaro, Alkassoum Indattou; Ministan Harkokin Cikin Gida, Alkache Alhada; Ilimi, Mamoudou Djibo; Harkokin Waje, Kassoum Maman Moctar; Lafiya, Illiassou Idi Mainassara; Agaji da Kyautata Rayuwa, Laouan Magagi; Samar da Sana’o’i, Kassoum Maman Moctar sai kuma Ministan Kiwo kuma Kakakin Gwamnati, Tidjani Idrissa Abdoulkadri.

Sauran ministocin sun hada da Ministan Shari’a, Boubakar Hassan; Sadarwa, Zada ​​Mahamadou; Kudi, Ahmat Jidoud; Kasuwanci, Masana’antu da Sana’o’in Matasa, Gado Sabo Moctar; Noma, Alambedji Abba Issa; sai Ministan Tsare-tsare, Abdou Rabiou da sauransu.

Bazoum da Ministocin Gwamnatinsa, bayan taronsu na farko. (Hoto: @mohamed.bazoum)
%d bloggers like this: