An naɗa matashi Gabriel Attal mai shekaru 34 a matsayin sabon firaiministan Faransa, wanda shi ne mutum mafi karancin shekaru a tarihin Faransa da ya riƙe mukamin.
Wannan da na zuwa ne a ƙoƙarin shugaba Emmanuel Macron na farfado da gwamnatinsa domin inganta ayyukan gwamnatinsa.
- Gwamnatin Tarayya za ta kafa kwamitin yaƙi da digirin bogi
- An tura matashi gidan yari kan yi wa jaririya fyade
Mista Attal ya maye gurbin Elisabeth Borne wadda ta yi murbus bayan watanni 20 a kan kujerar.
A tsawon lokacinta, ta yi fama da rashin rinjaye a majalisar dokokin ƙasar, inda a bayan nan wasu rahotanni ke cewa ta yi murabus din ne saboda rashin goyon bayan sauye-sauyen da shugaba Macron ke yi a gwamnatinsa.
Gabriel Attal, wanda a yanzu haka shi ne ministan ilimin Faransa zai jagoranci gwamnati a yayin da ake shirin zaɓen ’yan majalisar dokokin Turai a cikin watan Yuni.
Ya kasance mutum na farko dan luwaɗi a bayyane da zai riƙe wannan muƙamin.
A zaɓen 2017 ne ya zama ɗan majalisar dokoki kuma ɗaya daga cikin ɗan ga-ni-kashe-nin Shugaba Macron.
A lokacin yana ɗan shekara 29, an ba shi muƙamin ƙaramin minista a ma’aikatar ilimi sannan a shekara ta 2020 ya zama kakakin gwamnati.
Bayan da shugaba Macron ya yi tazarce, sai aka naɗa shi ministan kasafin kuɗi kafin ya koma ministan Ilimi.