✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An masa daurin shekara 6 saboda noma tabar wiwi

Alkalin ta yanke masa da hukuncin bayan samun sa da laifi noma da kuma ta'ammali da tabar wiwi

Babbar kotun tarayya da ke Ibadan ta yanke wa wani manomi hukuncin daurin shekara shida kan laifin noma da kuma ta’ammali da tabar wiwi.

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), ce ta gurfanar da manonmin bisa tuhume-tuhume biyu da suka hada da noma da kuma ta’amalli da miyagun kwayoyin.

Mai shari’a A. Okeke ce ta yanke masa huukuncin daurin shekara 6 ne bayan lauya mai shigar da kara, Misis Anne Balogun ta gabatar da shi.

Okeke ta yanke masa hukuncin daurin shekara uku kan laifin noma rabin hekta na tabar wiwi a kauyen Ibu-Ade da ke Apata a Ibadan.

Ta kuma sake daure shi na shekara uku kan laifin safarar kilogiram 64 na tabar, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito.

Alkalin ta ce “Na yanke masa hukuncin daurin shekara uku a kan laifi na daya da kuma daurin shekara uku a kan laifi na biyu. Hukuncin zai fara aiki a lokaci guda daga ranar da aka kama,” in ji ta.

NAN ta ruwaito cewa alkalin ta kuma umarci NDLEA da ta lalata abubuwan da aka kama idan ba a daukaka kara a cikin kwanaki 30 ba.

Tun da farko dai lauyan mai shigar da kara ya shaida wa kotun cewa an kama wanda ake tuhumar ne a ranar 12 ga watan Satumba a kauyen Ibu-Ade bisa zargin yin noma da kuma yin mu’amala da tabar wiwi.

Ta kira jami’in NDLEA, Olaniyan Olutayo a matsayin shaida, wanda ya kawo tabar wiwi mai nauyin kilo 64 a matsayin hujja.

Lauyan wanda ake kara, Mista Adetola Babalola, ya roki da a yi masa sassauci wajen yanke masa hukunci.