Wata Kungiyar mata a Kasar Faransa ta maka masu shirya gasar sarauniyar kyau a kasar a kotu saboda zargin nuna wariya da bambamci.
Kungiyar ta ce an nuna bambanci wajen zaben masu shiga gasar, abin da ta ce bai yi mata dadi ba, don haka za ta tafi kotu domin a bi musu kadinsu a gaban kuliya manta sabo.
- Jiragen yaki Super Tucano 12 da Buhari ya sayo sun iso Najeriya
- Majalisa za ta amince da kasafin kudin badi a watan Dasumba
Kungiyar tare da wasu ’yan mata uku da aka hana shiga gasar sun ce za su gurfanar da kamfanin shirya gasar tare da kafofin talabijin da ke taimaka wa shirin.
Masu karar sun ce masu shirya gasar na saba wa dokokin hana nuna bambamci a kasar wajen cewa dole sai tsayin ’yan takarar ya kai mita 1.7, kuma su kasance marasa aure, sannan kyawawa.
Tuni aka shigar da karar a wata kotu da ke wajen birnin Paris.