Wasu iyalai sun maka kamfanin Google a kotu bayan ɗansu ya faɗa karyayyar gada da mota ya mutu, sanadiyyar bin kwatancen ‘Google map’.
Iyalan, wadanda mazauna birnin North Carolina ne na kasar Amurka sun kai karar kamfanin suna zarginsa da yin sakaci.
- Ban ga dalilin da ’yan Najeriya za su rika rayuwa cikin talauci ba – Tinubu
- Tinubu ya dawo da tallafin mai
Philip Paxton, wani ma’aikacin lafiya kuma mai ’ya’ya biyu dai ya nitse ne a cikin ruwa a watan Satumbar bara, bayan motar da yake tuƙawa ta faɗa cikin ruwa daga gadar da ta karye shekara tara da suka wuce.
A cikin karar da suka shigar ranar Talata, iyalan mamacin sun yi korafin cewa mutane da dama sun ankarar da kamfanin cewa gadar ta karye saboda ya gyara kwatancensa a kan hanyar, amma ya ki.
A lokacin dai Philip ya tuƙa motar ce da daddare, sannan ya faɗa cikin wani rafi mai zurfin kafa 20, saboda bai san gadar ta karye ba.
Masu bayar da agajin gaggawa dai a lokacin sun tsinto motar marigayin ta kifa (sama a ƙasa) kuma ta nitse a cikin ruwan.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake zargin kamfanin na Google da zama ummul-aba’isun yin kantafi da rayuwar masu amfani da shi ba ta hanyar yi gurgun kwatance.