Wata mata mai shekara 30, Yinka Afolabi, ta gurfana a gaban wata kotun majistare da ke yankin Iyaganku a Ibadan a Jihar Oyo, bisa zarginta da cin zarafin ’yan sanda.
An tuhumi matar ne da laifin haɗa baki tare da tayar da tarzoma.
- Harin Isra’ila Ya Tilasta Rufe Asibitin Gaza
- Buratai ya bukaci sojoji su gaggauta murkushe ’yan ta’addanci
Sai dai wadda ake tuhumar ta musanta zargin da ake mata.
Ɗan sanda mai shigar da ƙara, Oladejo Balogun, ya shaida wa kotun cewa wadda ake tuhumar ta aikata laifin ne da misalin ƙarfe 10:30 na safiyar ranar 27 ga watan Mayu, 2024 a unguwar Elebu a Ibadan.
Balogun, ya ce Afolabi ta tara mutane domin su farmaki wasu jami’an ’yan sanda da ke bakin aiki a yankin.
Mai gabatar da ƙara ya bayyana cewa wadda ake ƙarar ta bijire wa jami’an ’yan sandan da suka yi ƙoƙarin tafiya da ita.
Ya ce laifukan sun ci karo da sashe na 516 da na 249 (d) na dokokin laifuka na Jihar Oyo.
Alƙalin kotun, Misis Olasinmibo Sanusi Zubair ta bayar da belin wadda ake ƙarar kan kuɗi Naira 100,000 tare da gabatar da mutum biyu da za su tsaya mata.
Ta kuma ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 6 ga watan Yuni, 2024.