Wata Babbar Kotun Jihar Kano, ta sanya ranar 11 ga watan Yuli, 2024 don fara sauraron ƙarar da jagoran jami’yyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso da wasu mutum bakwai suka shigar da EFCC.
Waɗanda suka shigar da ƙarar sun hada da jam’iyyar NNPP, Dokta Ajuji Ahmed, Dipo Olayanku, Ahmed Balewa, Chief Clement Anele, Lady Folshade Aliu, Buba Galadima da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
- HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar surukar Ganduje a Kano
- Tsige Sarkin Musulmi: Shettima ya gargadi Gwamnan Sakkwato
Kwankwaso da sauran mutanen sun shigar da ƙarar Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC) a kotu.
Bayan gabatar da ƙarar a gaban mai shari’a Yusuf Ubale Muhammad a ranar Litinin, lauyan masu ƙara, Barista Robert Hon, ya bayyana wa kotun cewa sun shaida wa waɗanda suke ƙara game da shari’ar a ranar 10 ga watan Yuni.
Amma a cewarsa ba su bayyana a kotu ba kuma ba su aike da wata takarda ba.
A nasa ɓangaren, alƙalin ya ce ya kamata a bai wa waɗanda ake kara isasshen lokaci domin su yi martani.
Saboda haka ya ɗage sauraren ƙarar zuwa ranar 11 ga watan Yuli, 2024 domin ci gaba da shari’ar.
Aminiya ta ruwaito cewa kotu ta hana EFCC cin zarafi, tsoratarwa, kamawa ko musgunawa masu ƙarar har zuwa lokacin da za a ta saurari shari’ar.