More Podcasts
A ranar Litinin 25 ga watan nan na Nuwamba ne kotu ta yanke hukunci kan ƙarar da wasu lauyoyi suka shigar kan harin da jirgin rundunar sojan sama ta Najeriya ya kai wa masu taron Maulidi a kauyen Tudun Biri da ke Ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar kaduna.
Idan masu saurare ba su manta ba, harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 100, baya da wasu a dama da suka ji munanan raunuka.
Sai dai a hukuncin da kotun ta yanke, ta kori ƙaran da lauyoyin suka shigar, saboda rashin shigar da ƙarar yadda ya kamata.
- NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da CNG
- DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi duba ne kan hukuncin da kotu ta yanke kan al’ummar ƙauyen Tudun Biri.
Domin sauke shirin, latsa nan