✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An maka Hafsat Idris a kotu saboda kin fitowa a fim din da ta karbi N1m

Kamfanin dai na zargin jarumar, wacce aka fi sani da ‘Barauniya’, da saba alkawari.

Wani kamfanin fina-finan Hausa, UK Entertainment, ya maka fitacciyar jarumar nan a masana’antar Kannywood, Hafsat Idris, a gaban kotu saboda saba alkawari.

Kamfanin dai na zargin jarumar, wacce aka fi sani da ‘Barauniya’, da karbar kudi har Naira miliyan daya da dubu dari uku don fitowa a wani shirinsu mai dogon zango, amma ta ki cika alkawari.

A karar da kamfanin ya shigar gaban Babbar Kotun Kano mai lamba 14 da ke zamanta a Karamar Hukumar Ungogo, ya nemi kotun ta tilasta wa Barauniya ta biya su Naira miliyan 10 a matsayin diyyar asarar da ta sa suka tafka.

Kamfanin ya yi zargin cewa saba alkawarin ba karamar asara ya jawo musu tafkawa ba.

Sai dai wacce ake karar, ta bakin lauyanta, ta amsa tuhumar da ake yi mata kan aikata laifin.

Daga bisani dai kotun ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa wani lokaci a nan gaba.