Ranar Asabar ta karshen satin da ya gabata ce aka kammala gasar sukuwar dawaki da aka saba yi a duk shekara a filin sukuwa da ke unguwar sabon gida da ke kan hanyar Jibiya. An kwashe sati biyu ana gudanar da wannan gasa inda aka lashe kyaututtuka daban-daban kafin wannan rana.
Kamar yadda shugaban kungiyar sukuwar dawaki na Jihar Katsina, Majidadin Katsina Alhaji Abdu Usman wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Alhaji Aliyu Chindo ya shaidawa Aminiya, an sanya motoci 4 ne da aka lashe a wannan gasar kamar yadda aka saba.
Akwai mota da Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Farouk Umar Farouk ya sanya, sai motar mai girma Gwamnan Katsina Barista Ibrahim Shema da motar Mad Air ta Alhaji Alhaji Dahiru Mangal,sai kuma babbar mota wadda kuma ita ce babbar kyautar gasar wato motar mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumminu Kabir Usman.
Mahalarta gasar sun fito ne daga Jihohin Kano da Kaduna da Sakkwato da sauransu. Sannan an samu wadanda suka halarta daga kasashe irinsu Nijar da Ghana da makamantansu.
Alhaji Aliyu Chindo ya ce motar mai martaba sarkin Daura aka azawa mahaya sukuwar jahar Katsina yayin da ta Mad Air aka azawa mahayan da aka yiwa lakabi da dawakin Sudan yayin da sauran motoci na masu gasar ne da suka fito daga sauran wurare.
Doki mai suna Ci-mu-ci shine wanda ya lashe kyautar motar mai martaba sarkin Daura,Goldin Boy shine dokin da ya cinye motar Mad Air. Ita kuwa motar gwamnan jaha mahayan Fatima Stable na Kwamishinan matasa da wasanni na jahar akkwato ne suka yi nasarar lasheta. Free my soul shi ne dokin da ya yi nasarar lashe babbar kyauta ta motar Mai Martaba sarkin Katsina.
An lashe motoci hudu a gasar sukuwar dawaki a Katsina
Ranar Asabar ta karshen satin da ya gabata ce aka kammala gasar sukuwar dawaki da aka saba yi a duk shekara a filin sukuwa da…
