A ranar Talata da ta wuce ne Hukumar shirya kwallo a Afirka (CAF) ta bayar da sanarwar dage kasar Maroko daga daukar nauyin gasar cin kofin Afirka da zai gudana a badi idan Allah Ya kaimu.
Sai dai ya zuwa hada wannan rahoto, Hukumar ba ta ambaci kasar da za ta maye gurbin Maroko wajen daukar nauyin gasar ba.
Saboda haka yanzu Maroko ba za ta halarci gasar ba don ba ta daga cikin kasashen da za su fafata a gasar ko da an canza kasar da za ta dauki nauyi.
Ita dai Maroko tun farko ta aika da sakon koke ne ga Hukumar CAF na yiwuwar a dage gasar zuwa 2016 maimakon 2015 saboda matsalar yaduwar cutar Ebola a yankin Afirka amma Hukumar ta ki amincewa da batun kuma ta dibarwa kasar wa’adin zuwa ranar Asabar da ta wuce ko dai ta yanke shawarar daukar nauyin gasar ko kuma a kwace daga wajenta.
A ranar Talatar ce Hukumar ta karbe daga wajen Maroko bayan ta tabbatar Marokon ba ta da niyyar daukar nauyin gasar.
Tuni hukumar ta fara tuntubar kasashen da ke da shawa’ar daukar nauyin gasar, kuma nan da ’yan kwanaki za ta sanar sabuwar kasar da za a yi gasar a ciki.
Ana sa ran fara gasar cin kofin Afirka ne a ranar 18 ga watan Janairun badi.