✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘An kulle’ sojar da bidiyon neman aurenta da dan NYSC ya karade gari

Hukumomin sojin Najeriya sun kulle wata soja bayan bidiyonta da wani mai yi wa kasa hidima yana neman amincewarta domin ya aure ta ya karade…

Hukumomin sojin Najeriya sun kulle wata soja bayan bidiyonta da wani mai yi wa kasa hidima yana neman amincewarta domin ya aure ta ya karade gari.

Sojar ta samu shuhura a kafafen sada zumunta ne bayan yaduwar bidiyon, wanda a ciki aka ga mai yi wa kasar hidiman ya rusuna a kan gwiwarsa yana neman ta aure shi, ya kuma sanya mata zobe a dan yatsa.

A cikin bidiyon da aka yi a sansanin horas da masu yi wa kasa hidima, an ga wasu masu yi wa kasa hidima suna jinjina wa masoyan.

Kafar Econs Intelligence ta ruwaito cewa bayan bibiyar bidiyon, hukumomin soji sun gano jami’ar sun kuma tsare ta a wani sansanin soji da ke Ilori, Jihar Kwara, saboda zargin saba dokokin aiki.

Kawo yanzu hadai hukumomin soji da na Hukumar Kula da Masu Yi Wa Kasa Hidima (NYSC) ba su ce komai ba game da lamarin.

Abin dai ya faru ne a cikin makon nan mai karewa a lokacin bikin kamala samun horon masu yi wa kasa hidima da ke Yikpata, Jihar Kwara.