✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An Koya Wa Dalibai Mata Dabarun Yakar Cin Zarafi

An koya wa daibai mata hanyoyin kauce wa cin zarafi da kuma sabbin dabarun tsafta a lokacin jinin al'ada

An koya wa daibai mata a Jihar Borno hanyoyin kauce wa cin zarafi da ke barazana ga gare su da kuma sabbin dabarun tsafta a lokacin jinin al’ada.

A lokacin gangamin da  Gidauniyar Thalma Peace Foundation ta gudanar a Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Maiduguri, babban birnin jihar, jami’ar gidauniyar Fatima Mohammed Mafi, ta yi musu bayani a kan mahimmancin tsaftar jinin haila.

A jawabinta ga kungiyoyin da suka halarci taron, Rifkatu Lalai, ta bayyana cewa cin zarafi na jinsi da barazanar da mata ke fuskantakan jefa su cikin mawuyacin hali a mafi yawan lokuta .

Ta kuma karfafa gwiwar daliban da su tabbatar da sun kai rahoto ga hukumomi kuma kada su yi shiru kan faruwar wani lamari na cin zarafi, matukar ya taso.

Taron dai ya samu musayar ra’ayi tsakanin gidauniyar da daliban, inda aka karfafa wa daliban gwiwar su dage da karatunsu gami da tunatar da su game da makomarsu a matsayin jagorori a nan gaba.