✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kori manyan kwamandojin sojin Saudiya

A wani sauyin kuma na dabam, Saudiyya ta kori manyan kwamandojin sojinta ciki har da shugaban ma’aikata, a jerin matakan da masarautar ta dauka da…

A wani sauyin kuma na dabam, Saudiyya ta kori manyan kwamandojin sojinta ciki har da shugaban ma’aikata, a jerin matakan da masarautar ta dauka da tsakar dare.

BBC ta ruwaito cewa Sarki Salman ya maye gurbin manyan hafsoshin sojin kasa da na sama.

Kamfanin dillancin labaran kasar ne ya wallafa jerin sunayen mutanen da aka kora, amma ba a fadi dalilin sallamarsu ba.

Lamarin na faruwa ne a lokacin da yakin da ake yi a Yemen, inda Saudiyya ke jagorantar gamayyar rundunar yaki da masu tayar da kayar baya, ke shiga shekara ta uku.

An yi amannar cewar yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya Mohammed bin Salman, wanda shi ne ministan tsaron kasar, ne ke sa wa ana gudanar da sauye-sauye a kasar.

A bara dai, an daure fitattun ‘yan kasar Saudiyya a wani babban otal da ke Riyadh mai suna Ritz-Carlton, ciki har da shugabanni, ministoci da attajirai, a yunkurin da Mohammed bin Salman ke jagoranta na kawar da cin hanci da rashawa.