✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kori jami’in DSS daga aiki kan yin barazanar kisa

Jami'in ya yi barazanar kashe lauyan da adda.

Hukumar tsaro ta DSS ta kori jami’inta mai suna Alex Agbaeze daga aiki saboda barazanar kisa da ya yi wa Barista Chinedum Elechi a Umuahia, babban birnin Jihar Abia.

Lauyan da lamarin ya shafa shi ne Daraktan Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwanna na Jam’iyyar PDP na Jihar Abia.

Korarren jami’in ya aikata haka ne ranar Lahadi, 13 ga Nuwamban bara a hanyar Azikwe, inda ya yi barazanar kashe lauyan da adda.

Bayan korar sa daga aiki, an kuma mika shi ga ’yan sanda don fuskantar hukunci.

Da yake tsokaci kan batun, Barista Elechi ya yaba wa hukumar DSS kan matakin da ta dauka na korar jami’in don tabbatar da adalci.

Tuni dai an gurfanar da korarren jami’in a Kotun Majastare mai zamanta a Umuahia kan tuhuma uku da suka hada da yunkurin kisa da lalata dukiya da kuma cin zarafi.