✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kori dan sanda daga aiki kan satar waya

Jami'in dan sanda ya rasa aikinsa saboda zargin sa da satar wayar hannu da kudi N25,000

Wani dan sanda ya rasa aikinsa saboda zargin sa da satar wayar hannu da kudi N25,000.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Osun ta ce ta kori Felix Olayiwola ne bayan kama shi da laifin satar waya da darajarta ta kai N58,000.

Bayan korr sa daga aiki a ranar Litinin, Rundunar ta gurfananar da Felix a gaban Kotun Majistare bisa zargin yi wa wani matashi sata a garin Osogbo.

Wanda ake zargin ya musanta aikata laifin kuma lauyarsa, Mis Ope Oladele ta bukaci a bayar da shi beli.

Dan sanda mai gabatar da kara ya roki kuton kada ta bayar da belin wanda ake zargin saboda zai gudu.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Modupe Awodele ta bayar da beli a kan N100,000 da mutum biyu da za su tsaya masa.

Ta kuma dage sauraron shari’ar zuwa ranar 9 ga watan Nuwamba, 2020.