✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kori alkalan wasa 6 a Ghana har tsawon rayuwarsu

kungiyar Horar da Alkalan Wasa ta Ghana (RAG) a ranar Talatar da ta wuce ta bayar da sanarwar korar wadansu alkalan wasa shida da aka…

kungiyar Horar da Alkalan Wasa ta Ghana (RAG) a ranar Talatar da ta wuce ta bayar da sanarwar korar wadansu alkalan wasa shida da aka samu da laifin karbar toshiyar baki a lokacin da suke yin alkalanci.  kungiyar ta ce ta kori alkalan wasa ne har tsawon rayuwarsu.

Sannan kungiyar ta dakatar da wadansu alkalan wasa 47 na tsawon shekara 10 saboda samunsu da laifuffuka daban-daban da suka shafi cin hanci da rashawa.

Alkalan wasan da aka kora har abada, Hukumar kwallon kafa ta Ghana ta ce an yi musu haka ne bayan an same su da laifin karbar cin hanci da rashawa a wasannin da suka yi alkalanci.  Kuma wani dan jarida mai binciken kwakwaf dan asalin Ghana Anas Armaya’u Anas ne ya dauki hotunansu a asirce lokacin da suke karbar cin hanci ba tare da saninsu ba, inda ya sanar da kungiyar alkalan wasa ta Ghana, ita kuma ta gabatar da batun ga Hukumar Kula da kwallon kafa ta Ghana (FA) kafin Hukumar Kula da kwallon kafa a Afirka (CAF) ta shigo cikin batun.

Hukumar kwallon kafa ta Ghana ta kara da cewa, wadannan alkalan wasan da aka kora da wadanda aka dakatar na shekara goma, an yi musu haka ne bayan an kafa kwamitin bincike kuma aka same su da laifi. Kuma abin da suka aikata ya ci karo da dokar hukumar kwallon kafa ta Ghana da ta Nahiyar Afirka da ma ta duniya baki daya.

Idan za a tuna a watan jiya ma Hukumar kwallon kafa ta Ghana ta kori wadansu alkalan wasa biyu har tsawon rayuwarsu yayin da ta dakatar da wadansu 6 daga yin alkalanci tsawon shekara 10.

Yanzu adadin wadanda aka kora har iyakar rayuwarsu daga yin alkalanci ya karu zuwa 8 yayin da wadanda aka dakatar na tsawon shekara 10 ya karu zuwa 53 a Ghana.

Idan za a tuna kimanin mako biyu da suka wuce Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta dakatar da Mataimakin Kocin Super Eagles, Salisu Yusuf na tsawon shekara 1 saboda samunsa da karbar cin hanci da rashawa a lokacin da yake horar da kungiyar Super Eagles ta ’yan gida a wani faifan bidiyo da dan jarida Anas Armaya’u Anas dan asalin Ghana ya dauke shi lokacin da yake karbar cin hanci a Maroko ba tare da sanin kocin ba.

Hakan ya sa NFF ta kafa kwamitin bincike, kuma ta samu kocin da laifi inda ta dakatar da shi na tsawon shekara daya.