A ranar Alhamis din makon jiya ne wadansu matasa suka banka wa wani matashi mai kimanin shekara 27 mai suna Sulaiman Abdullahi wuta, ya kone kurmus bayan sun zarge shi da kashe abokinsa mai suna Tasi’u Tanko ta hanyar daba masa wuka a ciki.
Lamarin ya faru ne a Jagindi Gari da ke yankin Godogodo a karamar Hukumar Jama’a, Jihar Kaduna, inda aka ce lamarin ya faro ne a ranar Laraba da daddare bayan da takaddama ta hada Sulaiman da wani daban, shi kuma Tasi’u ya je shiga tsakani amma abokin nasa ya zaro wuka ya soka masa a ciki, kamar yadda Aminiya ta samu labari.
Lokacin da Aminiya ta ziyarci Jagindi Gari, mahaifin wanda aka soka wa wukar, ya shaida wa Aminiya cewa wannan lamari ya riga ya faru ya wuce domin na gida ne dukansu, don haka ya bar komai. “Ko da ’yan sanda suka same ni na shaida musu cewa ba na bukatar wata magana a kan lamarin don haka babu wani dan jarida da zan yi magana da shi.”
A gidan su Sulaiman, wakilinmu ya iske ’yan uwansa suna zaman makoki inda shakikinsa mai suna Muhammad Abdullahi, ya ce Sulaiman da Tasi’u abokai ne da a wani lokaci a daki daya suke kwana “Ko kafin faruwar lamarin a daren suna tare. Muna zaune da dadare sai aka zo aka ce ga Sulaiman can ya daba wa abokinsa wuka. Na isa wurin lokacin dan uwan nawa ya gudu da na ji ana cewa a nemo shi a kashe, sai na zame jiki na bar wurin kada rashin ganinsa ya sa a huce a kaina,” inji shi.
Ya ce, “Da na bincika sai na ji cewa fadan ma ba da shi suke yi ba, wanda dan uwana ya kashe ya je shiga tsakani ne kamar wasa sai ya ce ko za ka sayi fadan ne, kawai sai ya zaro wuka ya daba masa. Bayan ya gudu sai ya je ya boye a wani kango da gari ya waye sai ya shige cikin wani kwalbati, a nan ne wani ya gan shi ya fada wa wadansu matasa suka je suka dauko shi suna sara da dukansa za su kai shi wajen maigari, amma kafin su karaso sai wadansu suka ce a kashe shi kawai nan take aka zuba masa fetur aka kyasta masa ashana ya rasu.”
Ya ce ba su da wata magana tunda wanda ya kashe an ce hukuncinsa kisa ne, to shi ma an kashe shi. Ya ce abin da ya shaida wa ’yan sanda ke nan bayan sun kirawo su ofishinsu.
Da Aminiya ta tuntubi Sakataren kungiyar Jama’atu Nasril Islam na Kudancin Kaduna Alhaji Ilyasu Musa, ya jingina faruwar haka ne ga shaye-shaye da ke yi wa matasa katutu, inda ya yi kira iyaye da malamai da sauran jama’a su tashi tsaye wajen magance shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasa.