An kone gidan wani gwamna a sabon rikicin kabilanci da ya barke a Jihar Blue Nile da ke kasar Sudan
Rahotanni na cewa, rikici tsakanin Hausawa da kuma ‘yan kabilar Wad Al Mahi da su ke yi wa lakabi da gwarawa, ya sake kunno kai ne a wayewar garin ranar Talata.
An tashi da jin harbe-harbe a garin Damazin wanda ya watsu zuwa sauran garuruwa, inda Hausawan ke zargin gwarawan da kai musu hari, wanda hakan ta sa su daukar matakan kare kai.
A sakamakon sake barkewar rikicin, gwamnatin kasar ta cire gwamnan jihar, ta kuma nada wani a ranar Talata, wanda hotonsa ya ke ta yawo a dandalin sada zumunta.
Duk da wannan kokari da gwamnati ta ke yi, Hausawan na zargin hannun gwamnati a cikin rikicin, a matsayin wata dabara na ci gaba da mulki.
Hausawan dai na zargin cewa gwamnati ta ki dukar kwakkwaran mataki na shari’a a kan gwarawan da suka tayar da rikicin Damazin a watannin da ya wuce.
A cewar TRT World rikici tsakanin Hausawa da wasu kabilun kasar ya samo asali ne kan filin noma wanda ya ki ci ya kuma ki cinyewa.