A kasar Faransa, an kona akalla motoci 874 a jajiberin sabuwar shekarar 2022, a wata al’adar da aka jima ana sukarta.
Sai dai a bana, adadin ya ragu matuka, in aka kwatanta da guda 1,316 din da aka kona a 2019, kamar yadda Ministan Cikin Gidan Kasar Gerald Darmanin ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Asabar.
- Sojoji sun hallaka kasurgumin dan bindigar Zamfara, Alhaji Auta
- An rufe coci mai shekara 220 saboda karancin masu ibada
An dai rage yawan motocin ne saboda yawan ’yan sandan da suke kokarin tursasa jama’a bin matakan kariyar COVID-19, sakamakon samfurin Omicron mai saurin yaduwa da ya sake bulla.
Sai dai a bara, babu cikakken adadin motocin da aka kona saboda dokar kullen Corona.
Kamar a kasashe da dama dai, a Faransa ana kone motocin ne saboda masu aikata laifin da ke konawa don su bad-da-sahu da kuma masu yin ikirarin yin inshora na karya.
Sai dai a Faransa, lamarin ya dauki sabon salo, inda ake yi domin bikin sabuwar shekara.
Tarihi ya nuna cewa an fara bikin ne tsakanin matasa a yankin Strasbourg da ke Gabashin kasar a shekarun 1990.
Kazalika, an yi amfani da dabi’ar wajen yin zanga-zangar nuna fushin matasa kan wata dokar gine-gine a kasar a shekarar 2005.
A lokacin dai, ’yan sanda sun kirga kimanin motoci 8,810 da aka kona cikin kasa da mako uku.