An kuma kona masallatai da kuma hasarar dukiya a harin wanda ake zargin na ramuwar gayya ne da ake zargin ‘yan kabilar Tivi da kai wa Hausawa ko kuma Musulmi.
A ranar Talata ma an kashe mutum 17 ciki har da wasu limaman coci biyu.
Wadansu da suka ga lamarin sun shaida wa BBC cewa wadansu gungun mutane ne suka "tare hanyoyin cikin gari tare da tsare mutane, inda suka rinka doke su."
Rundunar ‘yan sandan jihar ta ki cewa uffan kan bukatar da BBC ta mata na yin magana kan lamarin. Shi ma sakataren yada labaran gwamantin jihar, Terve Akase, ya ce ba shi da labarin harin.
Sai dai wani Basarake na kabilar Tivi, wadanda aka zarga da kai harin, ya ce suna iya kokarinsu domin ganin ba a kai hare-haren ramuwar gayya ba.
Wani dalibi da ya shaida lamarin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce da idanunsa ya ga yadda gungun mutane suka "tare hanyar zuwa jami’ar garin kusa da wani asibiti suna tare mutane su doke su, kana kuma kuma su yi musu kwace."
Dalibin ya kara da cewa "Hausawa ne ko Musulmi ake yi wa hakan."