An jikkata mutane da dama tare da kona gidaje da shaguna a wani rikicin kabilanci a kan nadin sarauta a Karamar Hukumar Karim Lamido na Jihar Taraba.
Daruruwan mata da kananan yara sun tsere zuwa wasu wurare bayan barkewar rikicin a garin Karim Lamido, hedikwatar karamar hukumar.
- An kara kudin kujerar Hajji da $250
- An cafke dan shekara 80 cikin ’yan fashin da suka kashe dan sanda a Ibadan
Rikicin ya samo asali ne ‘yan kabilar Karimjo sun yi bore kan nadin da aka yi wa sabon basaraken garin daga kabilar Wurkum.
Matasan Karimjo, kabilar da ke da’awar su ne asalin ‘yan garin sun yi bore ne bayan dawowar sabon basaraken daga bikin mika masa sandar mulki da Gwamna Darius Ishaku ya yi.
Basaraken, wanda mahaifinsa ya rasu bayan sama da shekaru 40 a kan sarautar a watannin baya, yana daga cikin sarakunan gargajiya tara da gwamnan ya mika wa sandar mulki a Jalingo, hedikwatar jihar.
Sai dai dawowar basaraken daga bikin ke da wuya matasan Karimjo, da ke neman su ma a kafa masu masarauta amma ba su samu ba, suka fara gunaguni.
Boren, daga bisani ya rikide zuwa kone-konen gidaje da shaguna da kuma jikkata mutane da dama.
Daga baya dai an girke jami’an tsaro domin dawo da zaman lamfiya, kamar yadda kakakin ’yan sandan jihar, SP Usman Abdullahi ya shaida wa wakilinmu.
Shi ma daraktan yada labaran sojoji na jihar, Laftanar O. Oni ya ce an tura sojoji domin samar da tsaro a yankin, amma bai yi karin bayani ba.