Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Malam Kabiru Nakwango ya bayyana yadda ya sha fama da kiraye-kirayen waya da kuma jama’ar da ta yi tururuwa zuwa gidansa a lokacin da aka bayyana cewa ya mutu.
Wata jaridar intanet ce ta bayyana rasuwar jarumin a shafinta na Facebook a ranar Litinin.
- An ga ’yan bindiga da rana tsaka kan babura a cikin garin Katsina
- Rufe Jami’o’i: Gwamnati Ba Ta So Ta Yi Wa ASUU Karya —Abdullahi Adamu
A hirarsa da Aminiya Nakwango ya ce, yini ya yi yana amsa wayoyin mutanen da suke buguwa su ji gaskiyar labarin da jaridar ta yada na rasuwarsa.
“Na amsa waya ta fi dubu, daga karshe sai ba wa yarana wayoyin na yi, suka ci gaba da ba jama’a amsa saboda na gaji, aikin da na tafi in yi a gona ma ya faskara saboda damuna da waya”. In ji Jarumin.
Hakan ya tabbatar da kokarin da wakilinmu ya yi na magana da shi, amma duk lokacin da ya kira yaronsa ne ya ke dauka, sai wayewar garin Talata ya samu damar yin magana da shi baka-da-baka ta wayar tarho.
“Ka ga yanzun ma mutane ne cike a gidana suna ta zuwa min jaje, ina jin yau dai ba zan iya zuwa ko’ina ba.”
Jarumin ya yi fice a fina-finan Hausa a inda yake fitowa a matsayin babban matsayi na uba, ko Malami ko dattijo, ko kuma alkalin a inda yake birge mutane da iliminsa a addini.
Wannan ba shi ne karo na farko da ake yiwa jaruman fina-finan kagen labari maras dadi ba.
A kwanan baya an yiwa Dan Azumi Baba wanda aka fi sani da Kamaye karyar rashin lafiya, a inda ya yi alkawarin daukar mataki na shari’a