Jami’an kwamitin kar ta kwana kan yaki da annobar coronavirus a jihar Neja sun mika wani mutum da ya tsere daga Kano ya saci jiki ya shiga jihar ga cibiyar killace masu cutar COVID-19 da ke Minna.
Ana zargin mutumin, mai suna Mallam Yunusa Idris, yana dauke da cutar coronavirus don haka ya saci jiki ya shiga cikin jihar ta Neja inda ya wuce unguwar Zumba da ke karamar hukumar Shiroro ranar Talatar makon jiya.
Malam Yunusa direba ne ga Injiniya Mohammed Gumel, wanda ya rasu ranar Alhamis a Kano sanadiyyar rashin lafiyar da ba a tantance ba.
Malam Yunusa dai ya saci jiki ya shiga cikin unguwar ta Zumba ne a daren ranar Talata bayan addu’ar ukun mai gidan nasa.
Jin irin yanayin rasuwar mai gidan Malam Yunusa a Kano ya sa jama’ar yankin gaggawar sanar da jami’an hukumar kula da madatsar ruwa ta Shiroro da ’yan sandan yankin abin da ke faruwa.
Daga nan ne jami’an kiwon lafiya suka gayyaci Malam Yunusa don amsa tambayoyi, sai ya amsa cewa mai gidansa ya rasu ne bayan jinyar cutar da take da alaka da COVID-19, sannan ya yanke shawarar komawa garinsa na asali idan an yi addu’ar uku.
- An killace iyalan marigayi Sarkin Kaura Namoda
- Darussa uku da na koya a killace —Dan Atiku Abubakar
- Yadda na sha fama a killace har kwana 26 –El-Rufai
Ya kuma tabbatar da cewa, shi ne ya dauki mai gidan nasa a lokutan da yake rashin lafiya zuwa wani asibiti mai zaman kansa kafin ya rasu.
Jami’an da suke yaki da yaduwar cutar COVID-19 a jihar sun tura motar daukar marasa lafiya zuwa unguwar Zumba daga nan suka wuce da shi zuwa cibiyar da ake killace masu cutar coronavirus da ke Minna.
Bayan haka suka tura samfurinsa da suka dauka don a yi masa gwaji zuwa hedkwatar Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) da ke Abuja don sanin ko yana dauke da cutar.