‘Yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 42 a hare-hare daban-daban da suka kai ƙauyuka da dama a jihohin Zamfara da Katsina.
A Jihar Zamfara, an kashe mutum 12 da suka haɗa da ‘yan sanda bakwai a ranar Alhamis a ƙauyen Magarya da ke Ƙaramar Hukumar Zurmi.
Daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su har da wani jami’in ɗan banga a Jihar Zamfara, wanda aka fi sani da Askarawan Zamfara da wasu mazauna ƙauyen guda huɗu.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammad Shehu Dalijan, ya tabbatar wa Aminiya kisan jami’ansa da aka yi a daren jiya.
Rundunar ‘yan sandan ta ce ‘yan bindigar da yawansu ya kai 300, sun afka wa ƙauyen ne a kan babura.
“Sun kewaye jami’anmu ne suka buɗe musu wuta inda suka kashe bakwai daga cikinsu tare da jikkata wasu da dama.
“’Yan bindigar ba sa jin daɗin ayyukan jami’anmu da suke hana su aiwatar da ɗanyen aikin nasu sama da shekara biyu ba.
“Tun lokacin da aka tura ’yan sanda yankin, ‘yan bindigar ba su iya samun damar kai hari ƙauyen,” in ji Dalijan.
Kwamishinan ‘yan sandan ya ce za a ƙara yawan ‘yan sanda a yankin.
Wani mazaunin garin mai suna Muhammad Yusuf ya shaida wa Aminiya cewa, maharan sun mamaye ƙauyen ne da misalin ƙarfe 5:10 na safe a lokacin da jama’a ke shirin yin subhi (sallar asuba).
Ya ce, ‘yan bindigar sun kuma ƙona gidaje biyu, mota ƙaya da kuma manyan rumbunan ajiye abinci masu yawa.
“’Yan bindigan sun kuma yi awon gaba da raƙuma uku da wasu shanu, tumaki da awaki. Sai dai ba su yi awon gaba da kowa ba a yayin harin.
“Lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari ƙauyen, mutanen da ke cikin garin sun ruga cikin daji.
“Da kuma suka dawo, mun yi ƙidayar su, muka gano cewa an kashe mutane 12, ciki har da ‘yan sanda guda bakwai.
An kashe mutum 30, an jikkata wasu a Katsina
An kuma samu rahoton cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 30 a hare-haren da suka kai ƙauyukan ƙananan hukumomin Dutsinma da Safana na jihar Katsina.
Ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Tashar Kawai Mai Zurfi, Sabon Gari Unguwar Banza, Dogon Ruwa, Sanawar Kurecen Dutsi, Unguwar Bera, Kuricin Kulawa, Larabar Tashar Mangoro, Sabaru, Ashata, Unguwar Ido, Kanbiri, Kunamawar Mai Awaki da Kunamawar ‘Yargandu.
An ce an kai wa ƙauyukan hari ne a ranar Talata.
An ce ‘yan bindigar sun sake kai sabon hari a jiya a ƙauyukan Dogon Ruwa, ‘Yar Kuka, Rimi, Lezumawa da sauran ƙauyuka.
Hare-haren sun tilasta wa mazauna garin tserewa tare da neman mafaka a garin Dutsinma da ƙauyen Turare.