Shugaban riko na Karamar Hukumar Mubi ta Kudu, Ahmadu Dahiru da ke jihar Adamawa. Ya ce, wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe ‘yan sanda biyu da sace mutum bakwai a Karamar Hukumar.
Ahmadu, ya bayyanawa Kamfanin Dillancin Labarai NAN hakan a Gyela cewa, an kai harin ne a hanyar Mubi zuwa garin Gyela a ranar Talatar da ta gabata.
Shugaban ya kara da cewa, “Masu garkuwa da mutane ako da yaushe suna shiga garin dare da rana suna yin garkuwa da mutane kullum.”
Masu garkuwan sun kashe jami’an ‘yan sandan biyu da ke aiki a hanyar Mubi zuwa Gyela.