Jami’an tsaro karkashin rundunar tsaron hadin gwiwa ta musamman a Jihar Neja ta hallaka ’yan bindiga da dama da suka addabi Kananan Hukumomin Shiroro da Munya da ke Jihar.
Rahotanni sun ce hare-haren dai sun kuma yi sanadiyyar samun kubutar da dabbobi sama da 500 a yankunan Kuchi da Galadiman-Kogo da Allawa da kuma Erena da ke cikin Kananan Hukumomin biyu.
- Mutumin da ya fara tattaki daga Ingila zuwa Makkah don sauke farali ya isa Turkiyya
- Haramcin amfani da mutum-mutumi a Kano na nan daram – Hisbah
An dai kai dabbobin da aka kubutar din zuwa Minna, babban birnin Jihar a kan manyan motoci, tare da rakiyar mafarauta.
Sai dai biyar daga cikin shanun da aka ceto sun mutu a cikin motar da ta dauko su, saboda turmutsitsi.
A cewar Kwamishinan Kananan Hukumomi, Sarautun Gargajiya da Tsaron Cikin Gida na Jihar, Emmanuel Umar, dabbobin da aka ceto sun hada da shanu sama da 300 da tumaki sama da 100, kuma za su kasance ne karkashin kulawar Ma’aikatar Kula da Dabbobi ta Jihar.
Sai dai ya ce ko da yake an karkashe ’yan bindiga da yawa, su ma jami’an tsaron sun rasa wasu daga cikinsu, amma bai fadi adadi ba.
Amma ya ce akwai kyakkyawan shirin kula da iyalan jami’an da aka kashe din.
Emmanuel ya ce za a ci gaba da yin luguden wutar a kan dukkan bata-garin da ke Jihar, har sai an ga bayansu.
Ya kuma ce gwamnati zata ci gaba da ajiye dabbobin da aka kwato a hannunta, har sai masu su sun bayyana.