✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe ’yan bindiga 9 a hanyar Kaduna-Abuja

’Yan bindigar na kokarin tsallakawa wani sashe na hanyar ne lokacin da aka yi musu kwanton bauna

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce sojoji sun kashe ’yan bindiga tara biyo bayan wata musayar wuta da suka yi da su da sanyin safiyar ranar Talata a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Rahotanni sun ce sojojin sun sami nasarar ne bayan wasu rahotannin sirri da suka samu kan cewa ’yan bindigar na kokarin tsallakawa daga gabashi zuwa wani sashe na yammacin hanyar da wasu dimbin shanun da suka sata.

Kwamishinan Tsao da Al’amuran Cikin Gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan wanda ya tabbatar da hakan a wata sanarwa ranar Talata ya ce makiyayan da aka sacewa shanun ne suka ankarar da rundunar kan yunkurin maharan.

Dagan an ne a cewarsa su kuma ba ta yi wata-wata ba suka yi musu kwanton bauna tare da hallaka tara daga cikin sun an take.

Ya ce sojojin sun kuma sami nasarar kwace wata tankar yaki guda daya, bandir daya na kakin sojoji da takalmansu, barguna guda bakwai, wayoyin salula guda biyu, doguwar rigar guda daya sai igiyoyin daure shanun da dama.

Ya ce an kuma gano gawar wani dan bindiga guda daya, matattun shanu 16 da kuma wasu shanun guda uku dauke da raunuka a jikinsu.

A wani harin na daban kuma, Aruwan ya ce rundunar, tare da hadin gwiwar ’yan sanda ta dakile yunkurin wasu ’yan bindigar na guduwa da shanun sata a kan babbar hanyar, dab da Jami’ar Greenfield dake kusa da Kaduna.