✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe Uba da ’ya’yansa biyu a ƙauyen Filato

A cewar Jugo, an kashe mutanen ne cikin dare a lokacin da suke barci, inda ya bayyana lamarin a matsayin dabbanci.

Rahotanni sun ce an kashe wani uba da ‘ya’yansa biyu a ƙauyen Zogu da ke Gundumar Miango a Ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato.

Kakakin Ƙungiyar ci gaban Irigwe (IDA), Sam Jugo, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Jos, ya bayyana sunayen waɗanda harin ya rutsa da su kamar haka, Weyi Gebeh a mai shekara 56, da Zhu Weyi mai shekara 25 da Henry Weyi mai shekara 16.

A cewar Jugo, an kashe mutanen ne cikin dare a lokacin da suke barci, inda ya bayyana lamarin a matsayin dabbanci.

Ya ce, “An sanar da shugabannin Ƙungiyar ci gaban Irigwe (IDA) game da wani harin da aka kai ƙauyen Zogu, Miango wanda ya yi sanadin mutuwar wani uba da ‘ya’yansa biyu waɗanda suka haɗa da: Weyi Gebeh da Zhu Weyi da Henry Weyi.

“Wannan harin na baya-bayan nan ya kai ga mutuwar mutane tara a cikin makon nan kaɗai, Ƙungiyar IDA ta nuna rashin jin daɗinta game da taɓarɓarewar al’amura a yankin Irigwe tare da yin kira ga jami’an tsaro da su yi duk abin da ya kamata don daƙile wannan ɓarna a yankinmu tare da kama waɗanda suka aikata laifin don fuskantar shari’a.

Kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’ Manjo Samson Zhakom da rundunar ’yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, har yanzu ba su mayar da martani ga saƙon da wakilinmu ya aika masu ba.