Sojojin Jamhuriyar Nijar shida sun rasu a wani harin kwanton ɓauna da mayaƙa masu iƙirarin jihadi suka kai musu a ranar Lahadi.
Gwamnatin sojin Nijar ta ce a yayin musayar wutar, dakarun nata sun hallaka 10 daga cikin a mayaƙan da suka kawo musu farmakin a kan babura a garin Sanam da ke Jihar Tillaberi.
Shugaban gwamnatin sojin, Janar Abdourahamane Tchiani dai ya bayyana cewa sun yi wa Shugaba Mohamed Bazoum juyin mulki a ranar 26 ga watan Yuli ne saboda taɓarbarewar sha’anin tsaro a ƙasar.