Kwamandan yaki da Boko Haram, Janar Lucky Irabor ya sanar da cewa akalla sojoji 22 ne suka rasa rayukansu, sannan kuma kusan 75 suka jikkita a ci gaba da yaki da ake gwabzawa da Boko Haram a tafkin Chadi.
Kwamandan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a yau Alhamis, inda an yi wa rundunar sojin wannan ta’adin a sansanonin sojin kasar daban daban da ke yankin.
Hakanan kuma, kwamandan ya nuna cewa sun kashe kusan ‘yan ta’adda 59, sannan an kama guda takwas. Sannan kuma aka kwato makaman yaki da dama da suka hada da bama-bamai da bindigogi da sauransu.