An tabbatar da kashe mutum hudu da raunata wasu da dama a wani rikicin kabilanci tsakanin ’yan kabilar Tibi da na Ichen tare da kone gidaje a karamar hukumar Donga da ke Jihar Taraba.
Wasu wadanda suka tsallake rijiya da baya sun shaidawa Aminiya cewa, rigimar ta samo asali ne kan filin noma wanda ’yan kabilar Tibi da na Ichen ke ikirarin cewa nasu ne, amma daga bisabi matsalar ta rikide zuwa rikicin kabilanci.
Wani mazaunin garin Maraban Baissa, inda wannan lamari ya shafa mai suna Haruna Maraban Baissa ya shaidawa wakilin cewa, a garin Adamu ne rigimar ta fara daga nan kuma ta bazu zuwa Gwankwai da Maraban Baissa.
Ya ce, an kashe mutane masu yawan gaske kuma an kone gidaje masu yawa.
Haruna, ya ce ”A halin yanzu daukacin mazauna garuruwan uku sun tsere zuwa garuruwan Takum da Baissa domin gudun daukan fansa daga bangarorin da ke rigima da juna.“
- Iska ta hallaka mutum biyu ta lalata gidaje sama da 750 a Taraba
- An kashe mutum 15 a Taraba —’Yan sanda
- Taraba: Ana zaman zullumi a yankin Jukun
Ya kara da cewa, a halin da ake ciki yanzu wasu gidaje nacin wata kuma wasu maza da mata na dauke da kaya akan hanya kowa na neman masauki.
Kakakin rundunar ’yan sanda na jihar Taraba DSP David Misal, ya tabbatar da mutuwar mutum hudu a rikicin ’yan kabilar Tibi da Ichen a karamar hukumar Donga.
Ya ce, an tura jami’an ’yan sanda domin su kwantar da hankali a yankin.
A cewar DSP David, an sake tura karin ’yan sanda don hana daukan fansa daga bangarorin da ke rikicin kabilanci a yankin.