Mahara sun kashe mutum 70 a karamar hukumar Sabon Birni kwana daya bayan gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya kai ziyarar ta’aziya yankin.
Gwamnan dai ya je ta’aziyyar mutuwar wasu mutane 14 ne da maharan suka kashe ta hanyar yi wa wasu yankan rago a kauyen Gajit, ciki har da mai garin, ranar Sallah.
Abu kamar ya wuce za a dauki mataki sai ranar Laraba maharan suka yi wa wasu kauyukka biyar kawanya wadanda nisansu bai wuce kilomita biyar daga hedikwatar karamar hukumar ba.
Maharan, su fiye da 40 dauke da muggan makamai a kan babura, sun shiga kauyukkan ne da misalin karfe 3.00 na ranar Laraba, kuma ba su tambayi komai ba suka harbin kan mai uwa da wabi na tsawon lokaci, kamar yadda wata majiya a Sabon Birni ta shaida wa Aminiya a waya.
Majiyar ta kuma ce, “A yanzu da nake magana da kai, kusan duk mutanen da ke kauyukan Sabon Birni sun tashi don gudun wani harin, domin maharan sun sauya salon hari – a baya in sun zo dabbobinmu da kudade ne za su tafi da su, yanzu kuwa rayuwarmu suke nema.
‘Duk wanda ya hada ido da su…’
“Bayan maharan sun wuce da dare mutane suka shiga neman ’yan uwansu; zuwa yanzu an ga gawar mutane 70: a Garki 26, a Dan Aduwa 13, a Masawa 20, a Karine takwas, a Kazari uku.
“Wasu sun shiga daji neman ’yan uwansu zuwa yanzu ba su dawo ba, wadanda suka yi rauni ba a ma maganarsu [saboda] suna da yawa sosai.
“Akwai wadanda aka harba a bangarorin jiki da wadanda suka karye a kafa da samun rauni a jiki wajen tserar da rayuwarsu.
“A kan hanyarsu ta zuwa kauyukan, [maharani] sun yi ta harbe mutane – duk wanda ya hada ido da su sai sun kashe shi,” a cewar majiyar.
Har zuwa lokacin aiko da wannan rahoton rundunar ’yan sandan jihar Sakkwato ba ta ce komai a kan harin ba.