Akalla mutum biyar ne suka rasa rayukansu yayin wani rikici ya barke tsakanin manoma da makiyaya a Karamar Hukumar Imeko-Afon ta Jihar Ogun.
Gidaje da gonaki da babura da sauran kadarori da dama ne kuma aka banka wa wuta a yayin rikicin.
- An sake bude gidajen mai da kasuwannin shanun da aka rufe a Katsina
- AFCON 2021: Najeriya ta tsallake zuwa zagaye na biyu
Aminiya ta gano cewa rikicin na zuwa ne kasa da shekara daya bayan makamancinsa ya faru a yankin Yewa na Jihar.
Wakilinmu ya rawaito cewa rikicin ya fara ne ranar Laraba lokacin da makiyaya da wasu manoman Ohori suka fara taho-mu-gama da juna a kauyen Idofa, lamarin da ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.
Kazalika, mutanen yankin Aworo da ke Karamar Hukumar Yewa ta Arewa tun da farko sun fatattaki makiyaya daga kauyensu zuwa Idofa, inda suka kashe uku daga cikinsu sannan suka karkashe musu shanu.
Mazauna yankin na Aworo dai sun zargi makiyayan da lalata musu gonaki da hanyoyin samun ruwan shansu ta hanyar yin kiwo a fili, duk kuwa da haramta yin hakan da dokar Gwamnatin Jihar ta yi.
Sun dai shaida wa Aminiya cewa da yawa daga cikinsu sun gudu sun bar kauyukansu saboda tsoron ramuwar gayya.
Kakakin ’yan sandan Jihar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Asabar, amma ya ce ba su kai ga kama kowa ba tukunna.
A cewarsa, “Mum samu labari, kuma rikicin abin takaici ne. Mun kira dukkan bangarorin da lamarin ya shafa, ciki har da shugabannin Fulani na yankin, wadanda suka ce ba ma su da masaniya a kan harin.
“Muna ci gaba da bincike kuma za mu kama masu hannu a ciki don takaita ci gaba da yaduwar rikicin a nan gaba,” inji kakakin.