Gwamnatin kasar Turkiyya ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin bama-baman da aka kai a filin jirgin saman Ataturk da ke birnin Istanbul sun kai 41.
Gwamnan birnin ya ce 13 daga cikinsu ’yan kasashen waje ne, yana mai cewa mutum 239 ne suka jikkata.
Mahara uku ne a cikin motar tasi suka kai harin, inda suka bude wuta a kofar shiga filin jirgin ranar Talata, kamar yadda BBC ta bayyana.
Maharan sun tarwatsa kan su bayan ’yan sanda sun bude musu wuta.
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya dora alhakin harin kuna-bakin-wake da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 36 a filin jirgin birnin Santanbul, a kan kungiyar mayakan IS.
Ya ce an kai harin ne da manufar ba ta sunan Turkiyya a idanun duniya ta hanyar zubar da jinin mutane.
An tsayar da hada-hadar jirage sannan aka umarci mutane su kaurace wa filin jirgin.
Turkiyya dai na fuskantar hare-hare daga kungiyar IS da kuma mayakan sa-kai na kabilar kurdawa.
Wadannan hare-hare na zuwa ne a daidai lokacin da filin jirgin yake cike da jama’a.
A shekarar 2015 ne dai filin jirgin na Ataturk ya zamo uku ma fi yawan sauka da tashin jirage a nahiyar Turai.
Wato ya biyo bayan filin jirgin Heathrow da ke birnin Landan da na Charles de Gaulle na birnin Paris.
Fiye da fasinjoji miliyan 61 ne suka sauka ko suka tashi daga filin a bara.
An kashe mutum 41 a harin Turkiyya
Gwamnatin kasar Turkiyya ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin bama-baman da aka kai a filin jirgin saman Ataturk da ke birnin Istanbul…