✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 3 kan budurwa a Kwara

Rikicin ya barke ne bayan shugaban daya dabar ya kwace budurwar wani daga dabar abokan hamayyarsu

Mutum uku sun rasu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon rikicin da ya barke tsakanin wasu ’yan daba saboda budurwa a Karamar Hukumar Offa ta Jihar Kwara.

Wani ganau ya bayyana cewa an fara rikicin ne a ranar Asabar da dare, tsakanin gungun ’yan dabar Isale Oja da na Oja Oba a Offa.

“Kafin isar jami’anmu wurin da rikicin ya faru, an bindige mutum biyu har lahira, wato Samad Adeyemi, mai shekara 21, da Abdulahi Mohammed mai shekaru 20,” a cewar kakakin ’yan sandan Jihar Kwara, SP Ajayi Okasanmi.

Wani mazaunin yankin mai suna Alhaji Abdulrahman ya shaida wa wakilinmu cewa rikicin ya barke ne bayan daya daga cikin shugabannin dabar ya kwace budurwar wani dan adawarsu, wanda hakan bai yi wa abokan hamayyar tasu dadi ba.

A kana haka ne aka shiga ba wa hamata iska, har ta kai ga kisan kai.

Kakakin ’yan sandan jihar ya bayyana cewa an fara gudanar da bincike kan batun.