Dubun wani ɗan daba da ƙwacen waya da satar babura a cikin shigar mata mata wajen aikata ayyukan laifinsa a unguwar Ɗorayi da ke Jihar Kano ta cika.
An kama matashin mai suna Abdullahi, wanda aka fi sani da “Audu Manye,” ne bayan tsawon shekaru ana zargin sa da tunzura faɗan ’yan daba, fashi da makami da ƙwace wayoyi da satar babura a yankin.
Audu Manye ya shafe shekaru ya tsere wa jami’an tsaro ta hanyar yin shigar mata da hijabi da siket da da niƙabi, inda yake shiga cikin mata ba tare da an gane shi ba a yayin da yake aikata laifukansa.
Amma a ranar Laraba, dubunsa ta cika, inda haɗin gwiwar ƙungiyar “Gamayyar Matasan Kano,” tare da Kwamitin Tsaro na Al’ummar Ɗorayi, suka yi nasarar rutsa shi tare da kama shi.
- Mahara sanye da kayan ’yan sanda sun kashe malami sun sace mata 3 a makaranta a Zamfara
- Boko Haram ta ƙwace makaman sojoji na tiriliyoyin naira —Majalisa
Al’ummar Ɗorayi, waɗanda suka sha fama da yawan faɗan ’yan daba, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka, raunuka, da lalata dukiyoyi, sun nuna farin cikinsu game da kama ɗan fashin da ya addabe su.
Shugaban ƙungiyar matasan, Muhammad Tijjani Dorayi, ya bayyana wa wani shirin rediyo mai suna “Baba Suda,” cewa “Mun gano cewa wannan ɗan fashin yakan shiga unguwa ne a matsayin mace, sanye da hijabi, ba a gane shi. Da rana, yana harkokinsa kamar kowace mace, inda yake amfani da damar wajen aikata laifukansa ba tare da an gane shi ba.
“Tsawon lokaci, hukumomi sun yi ta neman sa, amma yana tserewa. Amma alhamdulillah ƙwazon matasanmu ya biya, a ƙarshe an kama shi kuma an miƙa shi ga ’yan sanda.”
Shugaban Kwamitin Tsaro na Al’ummar Dorayi, Malam Abdullahi Idris, ya bayyana cewa matashin ya daɗe a cikin jerin waɗanda suke nema ruwa a jallo.
Ya ce wanda ake zargin “yana ɗaya daga cikin fitattun ’yan fashin da suka addabi al’ummarmu. Salonsa na yin shigar mata, wanda ya sa da wuya a iya bibiyar shi, amma a ƙarshe da taimakon matasanmu, mun kama shi.”
Wani mazaunin yankin ya bayyana farin cikinsa da kama Audu Manye da cewa , “Mun daɗe muna rayuwa cikin tsoro saboda mutane irin su Audu Manye. Yakan yi shigar mace, ya shiga gidajen mutane, ya yi sata.
“Wani lokaci ma, yakan tunzura faɗa tsakanin ’yan daba, wanda yakan kai ga mutuwar mutane. Yawancinmu mun gane shi, amma ba mu iya tabbatarwa ba saboda shigarsa. Kama shi zai kawo mana sauƙi,” in ji shi.