Mahara sun kashe mutum 1,872 a Najeriya tare da sace wasu 714 daga watan Janairu zuwa Afrilun shekarar nan ta 2023, a cewar rahoton Gidauniyar Stefanos mai rajin kare hakkin dan Adam da wanzar da zaman lafiya.
Rahoton kungiyar mai zaman kanta ya kara da cewa an jikkata wasu mutum 65 a cikin wata hudun, inda ta bayyana damuwa kan yawan samun tashe-tashen hankula a Najeriya, du da cewa kasar ba a cikin yaki ta ke ba.
Shugabar wayar da kai a kungiyar, Fatima Njoku, ta yi kira ga hukuma da ta gaggauta daukar matakan maganance sabubban tashe-tashen hankula a Najeriya.
A taron manema labarai da kungiyar ta shirya a Abuja, Fatim Njoku ta ce, “Akwai tashin hankali, yadda ake bin talakawa da babu makami a hannunsu, har gida cikin tsakar dare a karkashe su da bindigogi da adduna, a kwashe dan abin da suke da shi, a kona kauyukansu.
- Boka ya yi tsafi da faston da ya je wajensa neman maganin ‘mu’ujiza’
- Yadda ’yan ta’adda suka kashe sojoji da ’yan sanda 967 a shekara 2
“Wani abin tashin hankalin shi ne ba a kama masu yin wannan barna, ballantana su fuskanci hukunci,” in ji ta.
Ta ce, “Bayanan da muka tattara daga shaidu daga sassan kasar nan sun nuna salon masu kai hare-haren kusan kusan iri daya ne, hakazalika yanayin mutane da suke kashewa.
“Hakan ya faru a yankunan Agatu, Guma, Logo na jihar Binuwai da kuma Kagoro, Zangon Kataf, Kajuru, Kafanchan a Jihar Kaduna, sai Bassa, Riyom, Barkin Ladi da kuma Mangu a Jihar Filato da dai sauransu.”
Da yake nasa jawabi a wurin taron, Shugaban Kungiyar Al’ummar Mwaghavul, Cif Joseph Gwankat, ya yi kira ga hukumomi da su hanzarta daukar matakan kawo karshen hare-haren da ake kai wa yankin.
Ya bayyana cewa tashe-tashen hankulan na dagula musu al’amura, sannan ya jaddada muhimmancin gwamnati ta magance matsalar daga tushe.