Rundunar ‘yan sanda a jihar Taraba ta ce an kashe mutane 15 a wani fadan kabilanci tsakanin ‘yan kabilar Shomo da Jole a karamar hukumar Lau.
Kakakin rundunar, DSP David Misal, ya shaida wa wakilin Aminiya cewa an kuma kone gidaje 100 a lokacin rikicin.
Binciken Aminiya ya gano cewa fadan ya barke ne a kan wani ruwa da ake kama kifi wanda kabilun biyu ke rigima a kan mallakarsa.
Taraba: Ana zaman zullumi a yankin Jukun
Coronavirus: Jama’a sun samu walwala a Jalingo
Rigingimu tsakanin kabilun biyu kan wannan ruwa sun jawo asarar rayuka masu yawan gaske.
Amma wata majiya ta shaida wa wakilin Aminiya cewa mutane 24 aka kashe a lokacin wannan mummunan fada.
Har yanzu kuma ba a gano wasu mutane masu yawan gaske da fadan ya rutsa da su ba.
Jihar ta Taraba dai na fama da rikice-rikicen kabilanci—ko a makon jiya ma sai da aka rasa rayuka a wani rikicin a tsakanin kabilun Tibi da Jukun.