Sabon rahoto na nuni da cewa akalla mutum 137 ne suka rasu sakamakon harin da aka kai wasu kauyuka da ke kan iyakar Jamhuriyar Nijar da kasar Mali.
Mayakan Boko Haram sun shiga kauyukan ne a kan babura, suna harbi kan mai uwa da wabi, inji kakakin gwamnatin kasar Abdoulraman Zakaria a ranar Talata.
- Mahara sun bindige mutum 40 a Nijar
- Gwamnatin Kano za ta gurfanar da mawakin yabo, Bashir Dandago
- Mutumin da yake sayar wa da ’yan bindiga babura ya shiga hannu a Kano
- Gwamnan CBN da Hafsan Sojan Kasa sun ki amsa gayyatar Majalisa
Sun kai harin ne a kauyukan Intazayene, Bakoarate, Wistane da kuma wasu makotan kauyuka.
A ranar Litinin sojojin Nijar sun gwabza kazamin fada tsakaninsu da mahara a yankin Tahoua, da ke kan iyakar kasar da Mali.
Harin ya yi sanadin mutuwar mutum 40, kamar yadda alkaluma suka nuna.
Amma a safiyar Talata sabon bincike ya gano adadin mutanen da suka rasun ya kai 137.
Ko a ranar 16 ga watan Maris, 2021, wasu mahara sun hallaka ’yan kasuwa 58 a yankin Tillaberi, kamar yadda sanarwar gwamnatin kasar ta bayyana.