✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe mutum 13, an yi garkuwa da 15 a Neja

Gwamna Bello ya yi alkawarin kawo karshen wannan ta’addancin da mutane ke fama da shi a jihar.

Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta bayyana cewa ’yan bindiga sun kashe mutum 13 a Karamar Hukumar Shiroro.

A ranar Lahadi ce kuma rundunar ta sanar da cewa ’yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutane 15 a kauyen Kulhu da ke Karamar Hukumar Mashegu.

Kakakin rundunar ’yan sandan, Wasiu Abiodun wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce maharan sun afka kauyen Kulhu ne da misalin karfe biyun dare suka kwashe mutane 15.

Abiodun ya kuma ce ’yan bindigar sun kwashi dabbobi masu yawa wanda har yanzu ba a iya tantance adadinsu ba.

Jaridar Premium Times ta ruwaito Abiodun yana karyata rahotanni da aka rika yadawa kan cewa mutum 32 ’yan bindigar suka kashe a harin da suka kai Shiroro.

Abiodun ya ce ’yan bindigar sun afka wa wasu manoma ne a gonakin su suna aiki a ranar Talatar makon jiya.

Bayan haka kuma Gwamna Abubakar Bello ya bayyana cewa wasu ’yan bindigar sun afka wa mutane a kauyen Wurukuchi duk a wannan hare-hare da suka kai.

Mai taimaka wa gwamnan jihar kan harkokin yada labarai Mary Noel-Berje, ta ce Gwamna Bello ya yi alhinin abin da ya faru a wadannan garuruwa sannan ya yi alkawarin gwamnati za ta kawo karshen wannan ta’addancin da mutane ke fama da shi a jihar.

Wasu alkalumma na baya-bayan nan sun nuna cewa a cikin shekara biyu ’yan bindiga sun raba akalla mutum 151,380 da matsugunan su wanda mafi yawan su manoma ne a Jihar Neja.

%d bloggers like this: