Mahara sun kaske akalla mutum 100 a lokaci guda a Karamar Hukumar Katsina-Ala ta Jihar Binuwai a ranakun Asabar da Lahadi.
Akalla gawarwaki 100 ne aka gano a yankunan da ’yan bindiga suka kai wa farmaki kamar yadda mahukunta suka bayyana.
- An kori hadimin Dan Majalisa saboda Shekau
- Jana’izar Janar Attahiru: Yadda Gwamnoni suka fusata ’yan Najeriya
Shugaban Karamar Hukumar Katsina-Ala, Alfred Atera, ya ce ’yan bindigar “Sun kashe sama da mutum 100 a wurare daban-daban, suna kashewa suna jefarwa a hanya, amma an gano wasu gawarwakin.”
Ya ce an kai hare-haren ne a gundumomin Mbayongo, Yooyo, Utange da kuma Mbatyula/Mbereve a lokaci guda.
Alfred ya ce mahara sun kori mutanen wani kauye a gundumar Yooyo, sannan ya yi zargin hadin bakin yaran tsohon shugaban ’yan ta’addan Jihar, Terwase Akwaza (Gana) da makiyaya wurin kai harin.
Shugaban Karamar Hukumar ya ce, jami’an tsaro na yin iya kokarinsu, amma maharan sun bullo da salon kai wa wurare daban-daban hari a lokaci guda ta yadda kafin a kai dauki sun yi barnarsu sun tafi.
Hadiminsa, Tertsea Benga, ya ce a ranar Asabar ’yan bindiga sun kai hari Mbayongo inda suka kona gidaje a kauyukan Vingir da Tse Nyipila da Tse Guji.
A ranar Lahadi kuma mahara sun kai hari a gundumar Mbatyula, inda daga baya aka gano gawarwaki da dama a yashe a cikin daji.
Mun yi kokarin samun karin bayani daga Jami’ar Hulda da Jama’a ta Rundunar ’Yan Sandan Jihar Binuwai, Catherine Anene, amma ba ta amsa kiran waya ko rubutaccen sakon da muka aika mata ba.