’Yan bindiga sun kashe wani manomi tare da sace wasu mutum 22 a kauyukan Dinki da Kidandan na Karamar Hukumar Igabi da Giwa a Jihar Kaduna.
Wani shugaban al’umma kusa da kauyen Dinki, Jafaru Anaba, ya bayyana cewa wasu mutanen kauyen sun bace a sakamakon harin.
- Badakala: Tinubu ya sa a binciki ministar Jin-kai, Betta Edu
- NAJERIYA A YAU: Dabarun Kauce Wa Talauci A Watan Janairu
Ya ce ’yan bindiga sun kewaye yankin, wanda hakan ya sa mazauna yankin cikin firgici.
Anaba ya ce, “Sun kai wa mutanen kauyenmu na Dinki hari a daren Asabar suka kashe mutum daya suka sace wasu kimanin 16.
“Har yanzu muna neman wasu da za su tabbatar da ainihin adadin wadanda aka sace.”
Ya ce duk da kokarin da dakarun soji ke yi a yankin, hakan bai hana maharan cin karensu ba babbaka ba.
A wani lamari kuma, an sace mutum shida a kauyen Kidandan da ke Karamar Hukumar Giwa a ranar Juma’a.
Sanusi Kidandan, wani shugaban al’umma, ya ce an sace mutanen kauyen biyar da misalin karfe 7:00 na yamma a wani wuri mai hatsari da ake kira Shalele.
Sai dai ya ce an garzaya da wani mutum da ’yan bindigar suka harba zuwa asibiti domin yi masa magani.
Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ’yan sandan jihar.
Kazalika, kakakin ’yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan bai amsa kiran wayar da aka masa ba.