An kashe manoma guda huɗu, tare da jikkata wasu a wani sabon hari da aka kai a wajen hakar ma’adanai a yankin Butura da ke ƙaramar hukumar Bokkos a Jihar Filato.
Lamarin ya faru ne da a daren ranar Alhamis da misalin ƙarfe 9 na dare.
- Son zuciya ne ya haifar da koma-bayan dimokuraɗiyya a Nijeriya – Sani GNPP
- Ahmed Musa ya koma Kano Pillars da ƙafar dama
Shugaban ƙungiyar matasan Butura, Sabastine Majit, ya tabbatar da faruwar harin a Jos, a ranar Asabar.
Ya bayyana sunayen waɗanda aka kashe: Bwefuk Musa, Klingshak Dickson, Promise Joshua da Nyam Abaka.
Ya kuma ƙara da cewa waɗanda suka kai harin sun gudu kafin zuwan jami’an tsaro.
Majit, ya bayyana cewa wannan hari ya faru ne kwanaki huɗu bayan aukuwar wani mummunan al’amari a ƙauyen Wumat, inda aka kashe mutane biyar ‘yan gida ɗaya, ciki har da wata mata mai juna biyu.
Ya ƙara da cewa a cikin wata ɗaya da ya gabata, an kashe sama da mutum 20 a yankinsu a sanadin hare-haren da ba a san dalilinsu ba.
Ya ce yankunan Barkin Ladi, Riyom, Bassa, Jos Arewa, Jos Kudu, Wase da Mangu, na ci gaba da fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda.
Majit ya ce idan hukumomi ba su ɗauki matakin kawo ƙarshen hare-haren ba, al’ummar yankin za su ɗauki makamai don kare kansu.