✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe makiyaya 2 da shanu 150 a sabon hari a Filato

A duk lokacin da aka kai mana hari, sai jami’an tsaro su nemi mu kwantar da hankalinmu.

Aƙalla makiyaya biyu da shanu 150 ne rahotanni suka ce wasu ‘yan bindiga sun kashe a wani hari da suka kai gundumar Kwal da ke Ƙaramar hukumar Bassa a Jihar Filato.

A cewar shugabannin Fulani a jihar, an kuma yi awon gaba da shanu sama da 100 a lokacin da lamarin ya faru.

Shuwagabannin Ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) da na takwararta Gan Allah Fulani (GAFDAN), Nura Abdullahi da Garba Abdullahi, sun tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin a ranar Juma’a.

Sun bayyana cewa akwai yiwuwar adadin shanun da aka kashe sun kai fiye da 150, yayin da wasu da dama suka ɓace.

Da yake bayyana lamarin, shugaban GAFDAN ya ce, “Makiyayan suna kiwon shanunsu ne da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar Laraba, kwatsam wasu ‘yan bindiga suka buɗe musu wuta.

“Sun harbe makiyaya biyu har lahira. Har ila yau, sun harbe ɗaruruwan shanu, inda suka kashe kimanin 150.

“Har yanzu ba mu tabbatar da yawan ɓarnar ba, domin lamarin ya faru ne a wani wuri mai nisa da ke da wahalar shiga, ba tare da jami’an tsaro ba. Mun yi babban rashi.

“Lokaci ya yi da jami’an tsaro za su ɗauki mataki kan ta’asar da ake yi wa mutanenmu.

 

“A duk lokacin da aka kai mana hari, sai jami’an tsaro su nemi mu kwantar da hankalinmu.

“Wannan yunƙuri ne na halaka mu, kasancewar hari ne na ba gaira ba dalili. Muna kira ga hukumomin tsaro da su kawo mana agaji.”

Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar wanzar da zaman lafiya ta ‘Operation Safe Haven’ a jihar, Manjo Samson Zhakom, sai dai haƙar ba ta cimma ruwa ba har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.