Wani fitaccen kwamandan ’yan banga a Jihar Kogi, Alhassan Alhassan, ya gamu da ajalinsa yayin wani artabu da ’yan bindiga a dajin Tanahu da ke Karamar Hukumar Kogi ta Jihar.
Wani dan banga da ya shaida abin da ya faru ya ce kwamandan ya jagorancin yaransa ne zuwa dajin don bankado maboyar ’yan bindigar da suka addabi kauyukan Aduho da Tanahu a yankin.
A cewarsa, da ganin ’yan bangar sai ’yan bindigar suka bude wuta, “An dauki lokaci ana artabu da su kuma a lokacin ne harsashinsu ya same shi”.
Ya ce nan take kwamandan ya fadi, ’yan bindigar suka tsere, shi kuma aka dauki gawarsa zuwa garinsu, Toto da ke Jihar Nasarawa, inda aka yi masa sutura kamar yadda addini ya tanadar.
Aminiya ta gano yadda marigayin da yaransa ke kai samame don dakile hare-haren ’yan bindiga da ke addabar matafiya a kan hanyar Toto zuwa Umaisha a Jihar Nasarawa.
Sarkin Gegu-Beki, Alhaji Mohmmed Abba Suleiman, ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho, a yayin tattaunawarsa da wakilinmu.
Kakakin ’yan sandan Jihar Kogi, CSP Williams Ovye Aya, bai amsa waya ko rubutaccen sakon da wakilinmu ya tura masa ba.