✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe kwamandan soja da wasu 16 a Binuwai

Wasu mahara sun hallaka wani kwamandan soji da wasu mutum 16 a wasu kauyuka uku da ke Karamar Hukumar Apa a Jihar Binuwai.

Wasu mahara sun hallaka wani kwamandan soji da wasu mutum 16 a wasu kauyuka uku da ke Karamar Hukumar Apa a Jihar Binuwai.

Mazauna sun shaida wa wakiliyarmu cewa an kashe kwamandan sojin da wani soja daya da fararen hula 15 ne a hare-haren da aka kai lokaci guda kusan Magariba, ranar Talata a kauyukan Opaha da Odogbo kuma Edikwu.

Wani mazaunin yankin mai suna Kole, ya ce a safiyar Laraba jami’an tsaro suka gano gawarwakin muyum 17 ciki har da na wasu sojoji biyu daga rundunar Operation Whirl Stroke (OPWS).

Ya ce daya daga cikin sojojin da aka kashe shi ne kwamandan rukunin sojojin da suka yi ba-a-kashi da ’yan bindigar da suka kai wa yankin hari.

Shugaban kungiyar cigaban al’ummar Apa, Baristta Eche Akpoko, ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma gano wasau  gawarwaki 10 da aka yi.
Kwamishinan Kudi na jihar, David Olofu, wanda dan asalin Opaha ne ya tabbatar da harin da kuma adadin gawarwakin da aka gano a ranar Laraba.
Mun nemi karin haske daga kakakin rundunar OPWS, DO Oquah, amma ya ce ya yi bulaguro, don haka ba zai iya yin bayani ba.
Haka ita ma kakakin ’yan sandan jihar, SP Catherine Anene, ta ce ba su samu rahoto ba.