Adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da aka kai a Jihar Binuwai ya ƙaru zuwa 72.
Adadin ya ƙaru ne bayan gano ƙarin gawarwaki 13 a ranar Litinin a ƙananan hukumomin Ukum da Logo.Adadin ya ƙaru ne bayan gano ƙarin gawarwaki 13 a ranar Litinin a ƙananan hukumomin Ukum da Logo.
Da farko a ranar Lahadi Gwamna Hyacinth Alia a yayin da yake jawabin Ista a wani coci, ya sanar a yayin cewa an gano gawarwaki 59.
Daga bisani aka gano ƙarin gawarwaki a cikin jejin yankunan da aka kai hare-haren.
- Motar hatsi ta kashe masu bikin Ista 5 a Gombe
- HOTUNA: An yi zanga-zangar adawa da matsalar tsaro a Filato
Kakakin gwamnan jihar, Isaac Uzaan, ya bayyana cewa an gano ƙarin gawarwaki 12 a Ƙaramar Hukumar Uku sauran mutum ɗaya kuma a Logo.
Tsakanin daren ranar Alhamis da safiyar Juma’a ne kai hare-hare a ƙauyukan yankin Sankera wanda ya ƙunshi ƙananan hukumar Ukum, Logo, and Kastina-Ala.