’Yan sanda sun hallaka wani kasurgumin mai garkuwa da mutane da ya addabi yankin babban birnin tarayya, Abuja.
An kashe fitaccen dan bindigan mai suna Isa Dei-Dei ne ranar Litinin a yayin artabu da jami’an tsaro da suka kai samame maboyar masu garkuwa da mutanen da suka addabi al’ummar yankin.
“Da suka hangi ’yan sandan sai suka fara guduwa, nan take jami’an suka bi su, lamarin da ya kai ga musayar wuta mai zafi, har aka kashe fitaccen dan bindiga Isa Dei-Dei,” in ji kakakin ’yan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi.
ACP Adejobi ya kuma sanar a safiyar yau Laraba cewa ragowar ’yan bindigar sun tsere da raunin harbin bindiga da suka samu a musayar wutar da jami’an tsaro.
Don haka ya roki jama’a musamman ma’aikatan lafiya da su sanar da jami’an tsaro idan suka ga wani da raunin harbin bindiga, domin a ci gaba da bincike.