✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe Janar ɗin soji a Abuja

Za a yi ƙoƙarin ganowa da kuma ɗaukar matakai kan waɗanda aka kama da aikata wannan ta’asar.

’Yan fashi da makami sun kashe wani janar ɗin soji mai ritaya a yayin harin da suka kai gidansa da ke rukununin gidaje na Sunshine Homes a unguwar Lokogoma a Abuja.

Rundunar ‘yan sandan Abuja ta bakin kakakinta, SP Adeh Josephine ta inganta rahoton da cewa jami’anta sun soma bincike dangane da kashe Birgediya Janar Uwem Udokwere a gidansa da ke babban birnin ƙasar.

SP Adeh Josephine ta bayyana cewa Kwamishinan ’yan sandan Abuja ya bayar da umarnin bin diddigin lamarin domin bankado miyagun da suka yi wannan mummunar aika-aika.

“Dangane da mummunan harin da aka kai rukunin gidajen Sunshine wanda ‘yan fashi da makami suka kai wanda ya yi sanadin mutuwar Birgediya Janar Uwam Harold Udokwere mai ritaya a ranar 22 ga watan Yunun 2024, da misalin 03:00 na asuba, kwamishinan ‘yan sandan birnin tarayya CP Beneth C. Igweh ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan yadda lamarin ya faru,” in ji sanarwar.

Kwamishinan ‘yan sandan ya jajanta wa iyalan mamacin inda ya ce za a yi ƙoƙarin ganowa da kuma ɗaukar matakai kan waɗanda aka kama da aikata wannan ta’asar.

Haka kuma kwamishinan ya jaddada cewa za su ci gaba da ƙoƙari wurin tabbatar da tsaro da kuma yaƙi da masu aikata muggan laifuka a birnin tarayyar.